1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Binciken tashin bamabamai a Kampala

July 23, 2010

Hukumomin leƙen asiri na ƙasashe na tura jami'ansu zuwa Uganda dangane ta hare-haren bom da aka fuskanta a ƙasar makonni biyu da suka wuce

https://p.dw.com/p/OSRL
A misalin makonni biyu da suka wuce an fuskanci tashin bamabamai a wurare uku a Kampalar UgandaHoto: AP

A dai kusan makonni biyu da suka wuce ne a daidai lokacin da mutane suka shagala wajen kallon wasan ƙarshe na gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta duniya birnin Kampalar Uganda bamabamai suka yi bindiga a wurare uku a babban birnin na ƙasar Uganda. A kuma wannan makon ba zato ba tsammani sai aka samu kutsen wasu jami'ai sama da sittin na 'yan sandan ciki na ƙasar Amirka FBI a birnin Kampala domin binciken wannan tsautsayi. A lokacin da take rawaito wannan rahoto jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

"Tuni dai birnin Kampala ya wayi gari a matsayin wani dandalin kutse na hukumomin leƙen asiri na ƙasashen ƙetare. A cikin cikakkiyar ɗamarar muggan makamai wasu dakarun 'yan sandan cikin Amirka na FBI suka kutsa birnin na Kampala domin binciken wuraren da aka kai hare-haren. Rahotanni ma sun nuna cewa ita ma Isra'ila ta tura jami'an hukumarta ta leƙen asiri Mossad a taƙaice zuwa Uganda a baya ga hukumar 'yan sandan ciki ta ƙasa da ƙasa da hukumar leƙen asiri ta Birtaniya da suka tura jami'ansu zuwa fadar mulkin ta Uganda. Gaba ɗaya dai an yi imanin cewar 'yan ƙunar baƙin wake ne ke da laifin hare-haren guda uku a Kampala kusan makonni biyu da suka wuce."

Uganda / Anschlag / Kampala
Mutane da dama suka samu rauni sakamakon hare-haren na ƙunar baƙin wakeHoto: AP

A dai halin da ake ciki yanzu ƙasashen Afirka na samun bunƙasar tattalin arziƙinsu duk da matsaloli iri daban-daban da suke fuskanta da kuma matsalar taɓarɓarewar al'amuran tattalin arziƙin duniya, a cewar jaridar Neues Deutschland. Jaridar ta ƙara da cewa:

"To sai dai kuma duk da gagarumar bunƙasar tattalin arziƙin da ƙasashen na Afirka ke samu har yau ba su fita daga ƙagin talauci da rashin aikin yi da yunwa da sauran matsalolin da suka saba addabar nahiyar Afirka ba."

Ita ma jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta lura da irin wannan ci gaba a nahiyar Afirka inda take cewa:

"Nahiyar Afirka tana daɗa zama dandalin zuba jari, inda masu zuba jari daga ƙetare suke sayyen hannayen jari, musamman a bankunan Afirka da kuma kamfanonin sadarwa waɗanda cin ƙazamar riba sakamakon bunƙasar da ake samu na masu amfani da wayar salula. Kazalika har ila yau ɗanyyun kayayyaki na taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasar tattalin arziƙin Afirka."

Luanda Angola
Ƙasashe da dama na Afirka na samun bunƙasar tattalin arziƙinsuHoto: picture-alliance / Jorn Stjerneklar / Impact Photos

Akan gwagwarmayar ɗora hannu kan albarkatun ƙasa da ɗanyyun kayayyaki a nahiyar Afirka ne jaridar Die Tageszeitung ta gabatar da wani rahoto inda take misali da ƙasar Kongo. Jaridar ta ce:

"Lardunan arewaci da kudancin Kivu dake gabashin Kongo suna samun kuɗaɗensu na shiga ne kacokam daga cinikin ɗanyyun kayayyaki, bayan shekaru kusan ashirin da suka yi suna fama da yaƙe-yaƙe. Ta cinikin waɗannan ɗanyyun kayayyki zuwa ƙetare ne suke da ikon shigo da ci-maka da kayan gini da makamashi da dai sauran abubuwan rayuwa ta yau da kullum. Wani kyakkyawan ci gaba da aka samu a wannan yanki shi ne koma bayan fasakwabrin ɗanyyun kayayyakin zuwa ƙasashe maƙobta ta yadda su kansu al'umar Kongo ne ke cin gajiyar lamarin. Ko da yake har yau akwai ƙungiyoyin tawaye da kan ɗauki matakai na ci da ceto akan al'uma."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi