Binciken makamai masu guba a Siriya | Labarai | DW | 05.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Binciken makamai masu guba a Siriya

Siriya ta bai wa masu binciken makamai na Majalisar Dinkin Duniya karin bayani a kan makamanta masu guba.

Majalisar Dinkin Duniya ta fadi cewar, gwamnatin kasar Siriya ta bai wa kwararrun masu binciken makamai na Majalisar Dinkin Duniya karin bayani dangane da shirin makaman na ta masu guba. Bayanan dai sun zarta wadanda tunda farko ta tanadar musu kafin ranar 21 ga Watan Satumban da ya gabata. Kakakin Majalisar Dinkin Duniya, Martin Nesirky, ya ce darekta janar na hukumar kare yaduwar makamai masu guba ta Majaisar Dinkin Duniya ya shaida wa kwamitin zartarwar hukumar cewar, gwamnatin kasar ta Siriya ta ba ta karin bayanai dangane da makaman na ta masu guba. Sai dai kakakin Majalisar ta Dinkin Duniya, bai bayar da wani karin bayani dangane da bayanan ba. A halin da ake ciki kuma, wata fafatawar da ta gudana kusa da kan iyakar Turkiya da Siriya, a tsakanin mayakan da ke da alaka da kungiyar alQa'ida da kuma Kurdawa - a wannan Jumma'ar, ta janyo mutuwar a kalla mutane 19. Masu fafutukar kawar da shugaba Assad daga mulki dai, na juyawa suna yakar junansu musamman a yankin arewacin kasar da kuma gabashi.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal