Binciken harin bam a Uganda | Labarai | DW | 13.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Binciken harin bam a Uganda

Gwamnatin Uganda ta cafke mutanen da take zargi sun janyo mutuwar masoya ƙwallo 74

default

Hukumomin ƙasar Uganda sun sanar da cafke wasu mutane bisa zargin suna da hannu wajen tada wasu tagwayen bama - baman da suka tarwatse a lokacin da wasu mutane ke kallon gasar ƙarshe ta cin kofin ƙwallon ƙafar da aka fafata tsakanin ƙasashen Spain da kuma Holland. Kakakin gwamnatin Uganda Fred Opolot ya bayyana cewar, da yammacin jiya Litinin ne suka yi nasarar cafke mutanen, tare da gano wani "Belt" irin na 'yan ƙunar baƙin waken da bai tarwatse ba a yankin Makindye dake Kampala, babban birnin ƙasar ta Uganda.

Tagwayen hare - haren biyu da ake dangantawa da ƙungiyar mayaƙan Somalia ta al-Shabab sun yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane 74 ya zuwa yanzu, a yayin da dama kuma ke ƙwance a asibiti ciki kuwa har da wasu Amirkawa da ke cikin jerin masu kallon ƙwallon a lokacin da matsalar ta afku. Tuni dai hukumomin na Uganda suka sha alwashin damƙo waɗanda ke da alhakin ƙaddamar da hare haren.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu