1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Wadatar abinciNa duniya

Illar abincin gwamgwami ga yara

Suleiman Babayo LMJ
December 3, 2025

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa yara a duniya suna cin abincin da aka gwangwani fiye da kima, abin da yake da illa a bangaren kiwon lafiya.

https://p.dw.com/p/54gvZ
Abincin da aka sarrafa
Abincin da aka sarrafaHoto: Michele Eve Sandberg/Sipa USA/picture alliance

Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya bayyana cewa kananan yara a duniya na cin abincin gwangwani da aka sarrafa da abubuwan da ke da illa a jikin dan Adam fiye da kima. Cikin wani sabon rahoto da asusun ya fitar ya ce, irin wadannan abinci da yara ke ci, na da matukar illa ga girman jikinsu da ma lafiyar kwakwalensu.

Binciken da aka yi

Rahoton ya ta'allaka ne da wani bincike da mujujallar kiwon lafiya ta The Lancet ta gudanar, wanda ya yi bayani dalla-dalla kan illolin da wadannan abincin gwangwani da aka sarrafa ke da su da mafi akasari suke dauke da siga da gishiri da kuma kitse da ke da illa ga lafiyar dan Adam.

Binciken da aka gudanar a wasu kasashe 11, ya nunar da cewa matsalar na shafar kaso 10 zuwa 35 na kananan yara 'yan shekaru biyar, yayin da ya kunshi kimanin kaso 60 cikin 100 na matasan da ke tasowa.