Bincike kan harbin ′yan jarida a Afghanistan | Labarai | DW | 04.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bincike kan harbin 'yan jarida a Afghanistan

Shugaba Hamid Karzai na Afghanistan ya nemi da ai bincike kan harbin da da aka yi wa wasu 'yan jarida biyu na kamfanin dillancin labarai na AP a kasar ta Afghanistan.

Wata sanarwa da fadar gwamnatin kasar ta fidda a wannan Juma'ar ta ce Mr. Karzai ya damu matuka da harbin da wani baturen 'yan sanda ya yi wa 'yan jarida wanda hakan ya yi ajalin daya yayin da gudan ta samu mummunan rauni.

'Yan jiridar biyu wato Anja Niedringhaus 'yar kasar Jamus da Kathy Gannon da ta fito daga Canada sun gamu da wannan ibtila'i ne lokacin da dan sandan ya bude musu wuta sa'ada da suke zaune cikin motarsu a wani yanki da ke gabashin kasar.

Tuni dai kamfanin dillancin labaran na AP da gwamatocin kasashen da 'yan jaridar suka fito suka yi Allah wadai da harbin da aka yi, tare da neman gwamnatin karsar ta hukunta wanda ya aikata wannan danyen aiki.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Pinado Abdu-Waba