Bikin ranar D-Day a Normandy na Faransa | Siyasa | DW | 06.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bikin ranar D-Day a Normandy na Faransa

Ranar 6 ga watan Yuni a Faransa, shugabannin manyan kasashen duniya suka yi bikin cika shekaru 70 da hada gwiwar sauka a Faransa lokacin yakin duniya na biyu.

Wannan mataki na hadin gwiwa ya zama tushen kawo karshen yakin. Wannan biki ya tunatar da ranar da sojojin Amrika suka sauka a Faranmsa, domin hada gwiwar yaki da rundunar mayakan Hitler na Jamus a nahiyar Turai. Umaru Aliyu yana dauke da karin bayani.

Daga cikin shugabannin da suka hallara domin gudanar da wannan biki na cikar shekaru 70 da saukar sojojin na Amirka a Faransa, ranar da ake kira D-Day, wato ranar yanke kudiri, har da shugaban Amirka Barack Obama da shugaban Rasha, Vladimir Putin da kuma Pirayim ministan Ingila, David Cameron. Ranar 6 ga watan Yuni na shekara ta 1944 sojoji kimanin dubu 160 na kasashen hadin gwiwa suka sauka a kasaar ta Faransa domin yaki da sojojin na Hitler, abin da masana suka ce ya taimaka domin domin gaggauta kawo karshen yakin duniya na biyu.Tun da asubahi aka fara wadannan bukukuwa tare da halartar wasu daga cikin sojojin da suke da rai har yanzu kuma suka shiga yakin. A jawabinsa a garin Caen, da yaki ya lalata, shugaban Faransa Francois Hollande mai masaaukin baki, ya tunatar da irin mummunan wahala da al'ummar nahiyar Turai suka fuskanta daga yakin, inda yace Faransawa kimanin dubu 20 ne suka rasa rayuknsu a ranar da sojojin na hadin gwiwa suka sauka a kasar da kuma 'yan makonnin da suka biyo baya.

Yace A wannan rana haske ya saukarwa Normandy, wanda kuma haske ne da har yanzu yake ci gaba da tabbata a nan. Sojoji fiye da dubu 150 daga Ingila da Amrika ne suka sauka a wannan rana a nan, cikin jiragen sama da kananan jirage masu saukar ungulu da sojojin laima domin su ceto mu.

Shugaban na Faransa yace kasarsa ba zata taba mantawa da irin abin da Amirka tayi mata ba. Yace a yau muna bikin ranar da ta zama abin tunawa, inda al'ummomi biyu suka kusanci juna, suka yi yaki na 'yantar da kansu da kuma duniya baki daya. Shugaban na Faransa da babban bako a wurin bikin, shugaban Amirka Barack Obama, sun ziyarci makabartan da aka rufe sojojin Amirka da aka kashe lokacin yakin kayar da rundunar mayakan Jamus. A jawabinsa a makabartar, shugaba Obama yace:

Nayi matukar farin cikin sake samun damar dawowa wannan wuri a yau, domin girmama mutanen da suka ki maida hankalinsu ga ko wane irin hadari dake tattare dasu. Daga cikinsu har akwai wadanda ke tare damu da suka yi wannan yaki. Ina jinjina maku ta hanyar kasancewata a nan .

Wani sojan Jamus mai suna Paul Golz yana dan shekaru 19 ne a ranar da sojojin na hadin gwiwa suka sauka a Normandy. Yace wannan al'amari har yanzu ya kasa mantawa dashi, ko da shike kamar yadda yace, ba wai saboda tsoron abin da zai sameshi ba ne, saboda a wannan lokaci, bashi da masaniya a game da abin da zai sameshi ko sauran takwarorinsa sojojin Jamus.

Yace a daidai wannan lokaci komai ya rikice, ba ma a rundunar mu kadai ba, amma har da su kansu sojojin rundunar ta hadin gwiwa saboda basu ma san inda suka sauka ba. Bugu da kari kuma rashin kyawun yanayin sararin samaniya ma ya taka muhimmiyar rawa, abin da ya sanyasojojin na kasashen hadin gwiwa duk suka watsu a kusa da inda muke, suna tsakaninmu, muna tsakaninsu, saboda haka ya zama tilas mu san yadda zasu bullowa wannan hali da muka tsinci kanmu a ciki.

A lokacin bukukuwan shugabanni sun tattauna halin da ake ciki a Ukraine, inda ma aka sami ganawa tsakanin shugaban Rasha, Vladimir Putin da sabon shugaban Ukraine, Petro Poroschenko.