1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Amirka ta dawo da tallafin Falisdinu

Ramatu Garba Baba
April 8, 2021

Shugaba Joe Biden ya sanar da dawo da tallafin da Amirka ke bai wa Falisdinawa bayan da tsohuwar gwamnatin Donald Trump ta dakatar da shirin a shekaru uku da suka gabata.

https://p.dw.com/p/3ri1T
APTOPIX Biden
Hoto: picture alliance / ASSOCIATED PRESS

Shugaban Amirka Joe Biden ya sanar da dawo da tallafin da kasar ke bai wa Falasdinawa. Shekaru uku bayan dakatar da tallafin kudin na shekara shekara da gwamnatin tsohon Shugaban Amirkan Donald Trump ta yi, gwamnatin Shugaba Biden ta sanar da dawo da bai wa Falasdinawan wannan tallafin da ya kai dala miliyan dari hudu (400) a duk shekara.

Gwamnatin ta Biden dai, ta ce ta dauki wannan matakin ne don karfafawa Falasdinawa guiwar komowa kan teburin tattaunawar zaman lafiya da makwabciyar kasar Isra'ila. Al'ummar yankin Falisdinu sun fuskanci kuncin rayuwa a tsawon wadannan shekarun da aka dakatar da tallafin kudaden ga yankin da ke fama da tashe-tashen hankula.