Bibi Titi Mohamed: ″Uwar kasa″ ta Tanzaniya | Tushen Afirka: mutanen da suka taka rawa a tarihin Afirka | DW | 20.08.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Tushen Afirka

Bibi Titi Mohamed: "Uwar kasa" ta Tanzaniya

Lokacin da Tanzaniya ta samu 'yanci Julius Nyerere ake dauka a matsayin uban kasa. Amma da ba domin Bibi Titi Mohamed, da ya rasa jigo wajen samun wannan nasarar.

A wane lokacin Bibi Titi Mohamed ta rayu?

An haifi Bibi Titi Mohamed a shekarar 1926 a tsakiyar Dar es Salaam ga iyaye Musulmai. Kamar sauran wadanda suka tashi tare ba su da ilimin boko, ta koyi abubuwa da dama daga iyaye da sauran dangi. A shekarun 1950 ta kasance cikin masu neman ganin Tangayika ta samu 'yanci daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya tare da mutane irin Julius Nyerere karkashin jam'iyyar kishin kasa ta Tanganyika African Nation Union wato TANU.

Ina Bibi Titi Mohamed ta samo sunanta?

Lokacin da Bibi Mohamed ta shiga fagen siyasa, ana mata lakani da "Titi" saboda girman jikinta da fadin kafada.

Shin da wani abu aka san Bibi Titi Mohamed?

Bibi Titi Mohamed ita ce mace ta farko da ta shiga gwagwarmayar neman 'yancin Tanganyika. A farko siyasarta ta janyo hankalin mata da dama domin shiga gwagwarmaya. A matsayin shugabar bangaren mata na jam'iyyar TANU, ita ce ke da alhakin shigar da mata gami da amincewa da manufofin jam'iyyar TANU.

Tashe da karshen Bibi Titi Mohamed!

Bayan Tanganyika ta samu 'yanci da kuma shekarun farko na kasar Tanzaniya, da hadaka tsakanin Tanganyika da Zanzibar, Bibi Titi ta rike mukamin minista a ma'aikatu dabam-dabam karkashin Shugaba Julius Nyerere. Amma kwatsam siyasarta ta kawo karshe lokacin da ta nuna rashin amince da manufofin gurguzu na Nyerere.

A dubi bidiyo 01:58

Bibi Titi Mohamed: "Uwar kasa" ta Tanzaniya

A shekarar 1969, an cafke Bibi Titi Mohamed, tare da mutane shida, da suka hada da ministan kwadago Michael Kamaliza gami da wasu hafsoshin soja bisa tuhumar yunkurin kifar da gwamnati. Ita da sauran da aka kama sun zama mutane na farko da suka fuskanci tuhumar cin amanar kasa. Bayana shari'a ta kwanaki 127, an yanke hukuncin rai da rai ga Bibi Mohamed. Amma an sake ta a shekarar 1972 (1977) bayan ahuwa ta shugaban kasa. Tun daga lokacin ta yi rayuwar kadaici daga iyalai da tsaffin abokai.

Yaya ake tunawa da Bibi Titi Mohamed?

Bayan ta raba gari da Julius Nyerere, yana da wuya a tattara bayanai game da Bibi Titi Mohamed. An dauki tsawon lokaci gwamnati ta yi shuru kan abubuwan da ta cimma. Wannan rashin nuna bayanai game da rawar da Bibi Titi Mohamed ta taka kan samun 'yancin Tanganyika ya zama rashin nuna taimakon da mata suka bayar, musamman a fagen siyasa baki daya.

Amma abubuwa sun sauya a shekarar 1991. Lokacin bikin cika shekaru 30 da samun 'yanci, jam'iyyar ta saka Bibi Titi Mohamed. A matsayin "Gwarzuwa na gwagwarmaya". Yanzu an saka sunanta a daya daga cikin manyan hanyoyi na birnin Dar es Salaam. 'Yan Tanzaniya da dama na tuna ta a matsayin "Uwar Kasa".

Wadanda ke taimaka da shawarwari wajen rubuta wannan tarihi sun hada da Farfesa Doulaye Konaté, Lily Mafela, da Farfesa Christopher Ogbogbo. Gidauniyar Gerda Henkel ce ta taimaka wajen kawo muku Tushen Afirka.

Sauti da bidiyo akan labarin