1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bernie Sanders ya shirya gogayya da Trump

February 19, 2019

Wani sanannen dan siyasar Amirka ya shirya fitowa don neman takarar shugaban kasar Amirka a zaben kasar da ke tafe.

https://p.dw.com/p/3Df6u
Florida, Bernie Sanders
Sanata Bernie SandersHoto: picture-alliance

Fitaccen dan siyasan nan na Amirka, Sanata Bernie Sanders, ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugabancin kasa a zaben 2020.

Mr. Sanders ya ce zai yi takarar ne saboda bayyana shugaba mai ci Donald Trump, a matsayin abin kunya ga Amirka.

Ya kuma bayyana Shugaba Trump a matsayin mai wariyar launin fata da kuma ke kokarin raba kan Amirkawa.

Senata Bernie Sanders dai shi ne ya sha kaye a hannun Hilary Clinton a fafatawar neman takara da suka yi a shekarar 2016.