1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Benny Gantz zai kafa gwamnatin Isra'ila

Mouhamadou Awal Balarabe
March 16, 2020

Madugun 'yan adawan Isra'Ila Benny Gantz ya samu izinin fara tattaunar share fagen kafa sabuwar gwamnati, kwanaki kalilan bayan zabuka na uku da aka gudanar a kasar cikin tsukin watanni 12 na baya-bayannan.

https://p.dw.com/p/3ZWAq
Benny Gantz
Hoto: Getty Images/AFP/G. Tibbon

Wata sanarwa da ta fito daga fadar shugaban kasar Isra'ila ta bayyana cewa 'yan majalisa 61 sun kada kuri'ar amincewa da Benny Gantz a matsayin wanda ya fi cancanta ya kafa sabuwar gwamnati, yayin da firaminita mai ci yanzu Benjamin Neatnyahu ya samu kuri'u 58. 

Wannan kaye da Firaminista Netanyahu ya sha bai zai kawo karshen mulkinsa ba, domin shugaban kasa Reuven Rivlin ya yi kira ga bangarorin da ke hamayya da juna da su kafa gwamnatin hadin gwiwa, domin kawo karshen rikicin siyasa da aka shafe watanni ana fuskanta a Isra'ila sakamakon rashin samun rinjaye a majalisa.

Babban kalubalen da ke gaban sabon majalisar ministocin Isra'ila dai shi ne annobar Corona wacce ta kama 'yan kasar 250.