1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila: Tuhuma kan Benjamin Netanyahu

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 2, 2019

Kotu a birnin Kudus ta fara sauraron shari'ar Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila dangane da batun cin hanci da aka jima ana dako.

https://p.dw.com/p/3QfJy
Israel Regierungsbildung | Benjamin Netanjahu & Reuven Rivlin
Fiaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na fuskantar kalubalen kafa gwamnati da gurfana gaban kuliyaHoto: Reuters/R. Zvulun

Wannan dai na zuwa ne jim kadan bayan zaben da har yanzu bai kammalu ba a Isra'ilan, sakamakon rashin samun cikakkiyar nasara ga duka 'yan takarar da za ta ba su damar kafa gwamnati. Zaben wanda aka gudanar da shi har sau biyu cikin shekara guda ba tare da samun nasarar kafa gwamnatin ba, ya sanya Firaminista Benjamin Netanyahu da ke zaman dan jam'iyya mai mulki ta Likud fafutukar ganin ya samu nasarar kafa gawamnatin hadaka domin kara tsawon wa'adin mulkinsa. Abokin hamayyarsa da suke tafiya kai da kai a wannan zabe da shi na jam'iyyar Blue and White Benny Gantz dai ya ki amincewa da hada kai da Natanyahu domin kafa gwamnatin hadakar, sakamakon zarge-zargen da ake wa Natanyahun dangane da cin hanci da rashin gaskiya da kuma zamba.