Beljiyam na neman zama makarfafar ′yan ta′adda | Siyasa | DW | 16.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Beljiyam na neman zama makarfafar 'yan ta'adda

Bayan hare-haren da aka kai Paris, al'ummar kasa da kasa ta fara sa ido a kan Beljiyam inda bayanan da ke fitowa a yanzu haka ke nuna cewa a can ne aka kitsa wannan harin.

Ba da dadewan nan ba ake kwatanta Beljiyam din a matsayin kasar da ke da matsalolin siyasa a cikin gida saboda rikicin da ke tsakanin manyan kabilun kasar na Flemmish da Waloof ko wanne na neman rinjaye. Sai dai yanzu da bincike ke nuna cewa yawancin wadanda suka kitsa wannan harin a beljiyam din suke zaune, ta fara samun sabon suna - makarfafan 'yan jihadi a Turai

Masana kimiyyar siyasa dai sun ce rashin kintsa gidanta ne ya janyo wannan matsala, domin kasar ta mayar da hankalinta ne kacokan kan matsalolinta ba tare da duba sauran abubuwan da ke faruwa ba, wanda ke nufin cewa matsalar ta sha karfinta a yanzu. To ko me mahukuntan kasar za su ce kan wannan batu? Ministan harkokin wajen Beljiyam Didier Reynders ya ce akwai matakan da suke dauka

"Ba wannan ne karon farko ba kuma mun san cewa ya kamata mu sake yin dammara, mu karfafa matakan da muka dauka a duk fadin Turai, amma ba mu kadai ba ne, akwai wannan matsalar a wasu biranen Turai ma, akwai a Faransa ma, amma kafin mun karfafa wadannan matakan, muna bukatar mu yi musayar bayanan sirri domin ba 'yan kasa daya ne kadai ba"

Alkaluma na nuna karuwar 'yan Turai a Iraki da Siriya

A cewar cibiyar nazarin tsatsaurar ra'ayi da tashe-tashen hankula na siyasa, (ICSR) mayakan jihadi wajen dubu 11 ne suka tafi kasashen Siriya da Iraki daga karshen shekara ta 2011 zuwa 2013, kuma mutun daya cikin biyar na wadannan 'yan jihadin daga yankin yammacin Turai suka fito. Alkaluman cibiyar na ICSR suna nuna cewa mayakan IS 296 daga kasar Beljiyam ne wanda ya sa su a kan gaba, wadanda ke da yawa kuma sai mayakan da suka yi mafari daga Jamus wadanda suka kai 240. Ga dai karin bayanin da ministan harkokin Faransar Didier Reynders ya yi:

"Akwai mayakan ketare sama da dubu 30 a kasashen Iraki da Siriya kuma a yanzu haka sun fito ne daga kasashe sama da 100. Saboda haka za mu cigaba da neman bayanan sirri kuma mu gudanarda bincike tare da tallafin mahukuntan Faransa, za dai mu fi bayar da fifiko ga musayar bayanan sirrin domin ta haka ne kawai za mu iya gano mutanen da ke da irin wannan tsatsaurar ra'ayin".

Musulmai a kasar Beljiyam suna da wata matsala kuma, wani bincike kuma da hadaddiyar kungiyar Turai ta yaki da wariya ta gudanar ya nuna cewa da wuya suke samun aikin yi. Kashi shidda cikin 100 na al'ummar musulmi ne, kuma ko da sun iya harshen kasar yadda ya kamata, duk da haka sai an nuna musu banbanci.

Yawaitan kungiyoyi masu akidu masu tsauri

Wata kungiya mai suna shari'a4Beljiyam ta rushe bayan da aka gudanarda shari'a mafi girma dangane da ta'addanci. An dakatar da kungiyar wadda ta dauki ma'aikata a hukumance sannan aka yanke hukuncin dauri na shekaru 12 wa shugabaninta. Sai dai a cewar sakataren da ke kula da harkokin Turai wannan matsala ce da ya kamata su yanke wasu shawarwari masu mahimmanci ba na musayar bayanai kadai ba

"Muna bukatar mun yanke shawarwari, muna bukatar hadin kai tsakanin 'yan sandan kasashen Turai da jami'oin shari'a domin mu yaki ta'addanci a kasar Turai, kuma mu yi amfani da shawarwarin da muka yanke bayan hare-haren da aka kai a watan Janairu inda Faransa tta ce za ta yaki sayar da makamai a Turai, da tallafawa 'yan ta'adda da ma kara inganta tsaro a cikin kasashe da ma yankin da yarjejeniyar Schnegen ke aiki"

Tun bayan hare-haren da aka yi a farkon wannan shekarar ta 2015 gwamnati Belijiyam ta ce ta zurfafa bincike har ma na kan wayoyin hannu amma duk da haka ana cigaba da samun matsala.

Sauti da bidiyo akan labarin