Bauchi: Matashiya mai sana’ar yin takalma | Himma dai Matasa | DW | 13.02.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Bauchi: Matashiya mai sana’ar yin takalma

Matashiyar mai suna Amina Adamu Koli ta bayyana cewa bukatar ganin ta samu abin dogaro da kanta shi ne dalilin da yasa ta fara wannan sana’a ta dinka jakkuna da takalma.

Wata matashiya da tayi karatu zuwa matakin difloma ta rike sana'ar dinka jakkuna da takalman mata da yara domin magance zaman kashe zani wadda zai taimaka mata don biyan bukatunta na rayuwa wadda yanzu haka sana'ar ta habaka har ta kai ga fara horas da wasu yan mata da matan aure irin wannan sana'a a karkashin ta.

Ko da yake Amina Adamu Koli tayi karatun ta har ta kammalashi, wadda kuma mafi akasarin matasa ire-irenta wadanda suka yi karatu sun fi raja'a da jiran sai gwamnati ta basu aikin yi wadda kuma a irin wannan lokaci yake da matukar wahalar samuwa, shin ko me yasa ita Amina ba ta tsaya jiran samun aikin gwamnatin ba.