Batun tsaro ya mamaye taron AU | Labarai | DW | 09.02.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Batun tsaro ya mamaye taron AU

Shugabannin kasashen Afirka da ke taron koli a Addis Ababa babban birnin kasar Ethiopia, sun yi alkawarin kara kaimi wajen warware matsalolin tsaron da suka dabaibaye nahiyar.

Yayin bude taron mai taken kawar da ayyukan 'yan bindiga don dorewar zaman lafiya a Afirka, shugaban hukumar tarayyar Afirkar, Moussa Faki Mahamat, ya lasafta matsaloli da dama da nahiyar ke a ciki.

Ya ce kasashen na fama da ta'addanci da matsaloli na bambance-bambancen kabila sai kuma wadanda ke tasowa a lokutan zabuka da ma bayansu.

Hankalin shugabannin na Afirka dai ya karkata yanzu ga batun samar da zaman lafiya, sama da sauye-sauye da ake fifitawa a baya, musamman batun cinikayya da zirga-zirga ba tare da shamaki ba a tsakaninsu.

Yanzu dai shugabancin kungiyar AU ya koma ga shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, bayan karewar wa'adin Abdel Fattah al-Sisi na Masar.

Shugancin kungiyar dai ana yinsa wa'adi daya na shekara guda.