1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Takun saka tsakanin Jamhuriyar Nijar da Turai

Salissou Boukari SB
March 13, 2026

Ministan kula da harkokin wajen Jamhuriyar Nijar, Bakary Yaou Sangaré, ya gayyaci mataimakiyar babban wakilin kungiyar Tarayyar Turai a Nijar Madame Nicoletta Avella, inda ya isar da bacin ran kasar.

https://p.dw.com/p/5AMRM
Mohamed Bazoum  tsohon shugaban Jamhuriyar Nijar
Mohamed Bazoum tsohon shugaban Jamhuriyar NijarHoto: Boureima Hama/AFP/AP/dpa/picture allaince

Ministan kula da harkokin wajen Jamhuriyar Nijar, Bakary Yaou Sangaré, ya gayyaci mataimakiyar babban wakilin kungiyar Tarayyar Turai a Nijar Madame Nicoletta Avella, inda ya isar da bacin ran kasar ta Nijar bayan amincewa da kudurin Majalisar ta Turai na neman a saki tsohon shugaban kasar Nijarvda aka hambare Mohamed Bazoum, bayan da ‘yan majalisar ta Turai kimanin 524 suka kada kuri'ar amincewa da kudirin neman a saki tsohon shugaban wanda ke tsare a fadar shugaban kasar na Nijar tun bayan juyin mulkin da akayi masa na ran 23 ga watan Yullin 2023. Tuni dai ake kallon wannan mataki a matsayin wani sabion babi nartikici tsakanin Nijar din da Tarayyar Turai. 

Daililin wannan kira

Kudirin da gungun biyar na siyasa na PPE, da ke a Majalisar ta Tarayyar Turai ya kada kuri'a a kai, na dauke da batutuwan cewa, tsohon shugaban kasar na Nijar Mohamed Bazoum, bashi da damar ganin lawya, ko samun wata ziyara ta ‘yan uwansa, inda ya kira duk kasashe mambobin kungiyar ta Turai da ma na Tarayyar Afrika, da sauran kasashen duniya da su yi matsin kaimi na diflomasiyya kan kasar ta Nijar don ganin an saki Bazoum din, wanda idan da yana kan karagar mulki wa'adin mulkinsa zai kare a ranar biyu ga watan Afrilu mai kamawa.

Majalisar mashawarta ta Jamhuriyar Nijar
Majalisar mashawarta ta Jamhuriyar NijarHoto: Salissou Boukari/DW

Sai dai yayin wannan kira da ministan harkokin wajen kasar ta Nijar ya yi wa wakiliyar ta Tarayyar Turai, ya damka mata wata wasika mai dauke da fushin kasar ta Nijar kan wannan mataki na Tarayyar Turai da suka kira na shishigi tare da yin Allah wadai da shi.

Sauran kasashen yankin

Ga bangarang kungiyar G25 da ke adawa da mulkin soja a kasar ta Nijar ta bakin mai magana da yawunta Tahirou Garka, ya ce wannan kira ko umarni na Tarayyar Turai na neman a saki tsohon shugaban kasa Mohamed Bazoum da sauran wadanda aka kama ba bisa ka'ida ba a cewarsa abin farin ciki ne inda ya yi kira ga sauran kungiyoyi da sunyi koyi da matakin naTarayyar Turai:

Janar Abdourahamane Tiani shugaban gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar
Janar Abdourahamane Tiani shugaban gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar NijarHoto: AFP

Sai dai ga masu sharhi kan siyasar kasa da kasa irin su Seidik Abba danjarida nakasa da kasa, na ganin cewa wannanwata guguwa ce da tatasoammakuma za ta kwata a a yi sulhu a ci gaba da hulda domintarayyar Turai na bukatar Sahel.

A baya dai ba da dadewa bay ayin wata ziyara da yakawo a Nijar da sauran kasashen AES, Wakili na musamman na kungiyar taTarayyar Turai a yankin Sahel ya sanar cewa da kungiyarsa taTarayyar Turai za ta gyara huldarta da kasashen na Sahel, said ai abun jira a gani shi ne ko wannan kutse na yan Majalisar na Turai ba zai iya mayar da hannun agogo baya ba.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani