Bashir mai sana′ar tura baro a Najeriya | NRS-Import | DW | 06.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Bashir mai sana'ar tura baro a Najeriya

Haduwar farko za ka dauka cewa Bashir ma’aikaci ne a daya daga cikin ofisoshi na gwamnati ko kamfani saboda yadda ya kure adaka ya yi gayu a lokacin aikin nasa na tura baro

A Najeriya wani mai sana’ar tura baro Bashir Sulaiman ya shiga jerin matasan da ke zama masu samar da sauyi a fanin daukan sana’asu da muhimmanci, saboda irin shigar da yake yi da ya sanya shi samun bunkasa a wannan sana’a da zama abin koyi da alfahari ga saura.

Bashir Sulaiman matashi ne mai shekaru 22 da haihuwa da ke sana’ar tura baro a kasuwar Utako da ke Abuja. Haduwar farko za ka dauka cewa Bashir ma’aikaci ne a daya daga cikin ofisoshi na gwamnati ko kamfani saboda yadda ya kure adaka ya yi gayu. Shin me ya dauki hankalinsa har ya shiga sana’ar tura baro duk da kwaliyar da yake yi?

"Abinda ya dauki hankalina na shiga aikin tura baro shi ne don in taimaka wa kaina ne in samu gudanar da rayuwata, don na ga abokaina da yawa suna zuwa su yi akin baro suna komawa gida, to sai na ce ni ma bari in zo don in samu yi wa kaina ba sai an yi mani ba. Yanzu haka ina da abokanin hulda guda 45 wadanda suke zuwa ina daukar masu kaya, kuma dukaninsu suna so na saboda hallaye masu kyau’

Bashir na cabawa a cikin sana'ar tura baro

Ga mafi yawan masu tura baro abin da sukan samu ba ya wuce Naira 700 a kowace rana, amma ga Bashir ya ce abin da yake samu ya zarta haka.

"To ni dai ina dan samun Naira 1500 zuwa 1800 haka amma daga ranar Jumma’a har zuwa Asabar nakan samu har Naira dubu uku zuwa Naira 3500 ina samu"

Amma Bashir kai ka fi zaben mutanen da suke tsaf-tsaf suka ci gayu don ka dauka masu kaya, me ya sa kai ka fi son irin wadannan mutanen ne?

"Saboda ba su da matsala dukkaninsu matasa ne don yanzu haka ba ni da abokin huldar da ta wuce shekaru 30 don ni ba na bin tsofafi idan ka bisu sun cika matsala".

Bashir na birge jama'a a cikin salon tafiyar da aikinsa

Ga Malam Hauwa Baba Ahmad da ke kungiyar talafa wa matasa su dogara da kansu ta bayyana tasirin da Bashir zai iya yi don zama abin koyi ga matasa.

"Matasanmu da yawa za ka iske su tura baro a matsayin sana’a abin gudu ne a wajensu, don suna ganinshi kamar kaskanci ne sana’ar tura baro. Amma a ce an samu wanda ya dauki sana’ar nan da muhimmanci har ya kasance ba za’a kyamace shi ba ga shi ya zama abin sha’awa ga mutanen da yake hulda da su wannan ai ba karamin abu ba ne. Akwai abubuwa da yawa da matasa za su koya, in har aka samu matasa biyu ko uku da suka dauki hallaye irin na Bashir to za’a samu canji"

Fatan Bashir Sulaiman ne ya ga cewa ya canza hallayan miliyoyin matasan Najeriya da Afrika su dauki sana’a da muhimmanci domin samar da sauyi a cikin al’umma, kamar yadda ta hanyar kasancewa cikin tsafta a sana’arsa ta tura baro Bashir ya samu bunkasa.