Siyasar Birtaniya na sake darewa
February 20, 2019Talla
Heidi Allen da Anna Soubry da Sarah Wollaston a wata wasikar hadin gwiwa da suka tura wa May sun ce gwamnatin May yadda take tafiyar da shirin fita daga Tarayyar Turai "cike yake da hadari" kuma jam'iyyar ta 'yan Conservative na hali na matsi saboda matakai masu tsauri na masu son fita daga Kungiyar EU.
A cewar 'yan majalisar dai tun bayan da aka cimma kuri'ar raba gardama kan fita daga EU a shekarar 2016, babu wani tartibin tsari na dinke baraka tsakanin 'yan jam'iyyar, ballantana samun hadin kai a mataki na kasa wajen aiwatar da shirin na Brexit.