AfDB ya nuna damuwa kan rancen da Afirka ke karba
March 13, 2024Talla
A yayin da yake magana da kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP a birnin Lagos na Najeriya, Akinwumi ya ce wannan tsari ba shi da kyau domin babu wata hanya da ake iya alkinta farashin albarkatun kasar da kasashen Afirka ke bai wa manyan kasashen na duniya wajen biyan basussukan da suka karba a irinwannan tsari.
Basussuka irin wannan ne dai ake gani suka zama dalilin karfin ikon da kasar China ta samu da wuraren hakar ma'adanai dabam-dabam na kasar Kongo, lamarin da ya kara jefa kasashen na Afirka cikin fatara.