1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

An nemi nada Muhammad Yunus shugaban gwamnatin Bangladesh

Suleiman Babayo USU
August 6, 2024

Masu zanga-zangar Bangladesh sun bukaci nada Muhammad Yunus mai bankin ba da bashi ga talakawa a matsayin jagoran gwamnatin wucin gadi, bayan tsohuwar firaministan kasar ta tsere saboda zanga-zangar da ta kifar da ita.

https://p.dw.com/p/4jAbQ
Bangladesh Muhammad Yunus
Muhammad Yunus masanin tattalin arziki na BangladeshHoto: Mahmud Hossain Opu/AP/picture alliance

Masu shirya zanga-zanga na kasar Bangladesh sun bukaci nada Muhammad Yunus masanin tattalin arziki a matsayin wanda zai jagoranci gwamnatin wucin gadin kasar, bayan da Firaminista Sheikh Hasina ta ajiye aiki kana tsare daga kasar zuwa Indiya, bayan zanga-zangar da aka kwashe makonni ana yi a kasar. Daya daga cikin shugabannin masu shirya zanga-zangar Nahid Islam ya bayyana bukatar ganin nada masanin tatalin arzikin ya jagoranci kasar.

Karin Bayani: Firaministar Bangladesh ta ajiye mukaminta

Shi dai Muhammad Yunus mai shekaru 84 da haihuwa ya yi fice a duniya saboda kafa bankin bai wa masu karamin karfi bashi a kasar Bangladesh, abin da ake gani ya taimaki milyoyin mutane a kasar wajen fita daga kangin talauci da kai yara zuwa manyan makarantu. Yunus ya kasance mai zuba jari kana masanin tattalin arziki a shekara ta 2006 ya samu lamban yabon Nobel na zaman lafiya saboda karamin bankin ba da bashi ga talakawa wanda ya kafa kuma ya zama abin koyi a sauran kasashen duniya.

Tuni dai Shugaba Mohammed Shahabuddin na kasar ta Bangladesh ya rusa majalisar dokokin kasar, abin da ya bude hanyar kafa sabuwar gwamnatin wucin gadi, kwana guda bayan Firaminista Sheikh Hasina ta yi murabus. A cikin wata sanarwa ofishin shugaban kasar ya fitar ya kuma bayyana kawo karshen daurin talala da tsohuwar gwamnatin ta take yi wa tsohuwar Firamnista Khaleda Zia, wadda ta kasance babbar mai adawa da Sheihk Hasina.