1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaBangladesh

Sakin babbari jagorar adawar Bangladesh

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 5, 2024

Shugaban kasar Bangladesh ya bayar da umurnin sakin babbar jagorar adawar kasar, sa'o'i kalilan bayan murabus din tsohuwar firaministar kasar Sheikh Hasina.

https://p.dw.com/p/4j8i6
Bangladesh | Adawa | BNP | Firaminista | Khaleda Zia
Tsohuwar firaministar Bangladesh kana babbar jagorar adawa Begum Khaleda ZiaHoto: A.M. Ahad/picture alliance/AP Photo

Shugaba Mohammed Shahabuddin na Bangladesh din dai, ya bayar da umurnin sakin tsohuwar firaministar kana shugabar babbar jam'iyyar adawar kasar ta (BNP) Begum Khaleda Zia. Sojoji ne dai suka kifar da gwamnatin Khaleda Zia da ke zaman babbar abokiyar adawar siyasar tsohuwar firaministar kasar da ta yi murabus, wato Sheikh Hasina. Shugaba Shahabuddin na Bangladesh dai, ya bayar da umurnin sakin Khaleda Zia ne jim kadan bayan murabus din Hasina.