Bangarorin palasdinawa na ci gaba da dauki ba dadi | Labarai | DW | 18.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bangarorin palasdinawa na ci gaba da dauki ba dadi

Duk da yarjejeniyar tsagaitawa da bude wuta da aka cimma a Gaza, rahotanni sun nunar da cewa har yanzu bangarorin palasdinawa na ci gaba da dauki ba dadi.

Bayanai sun shaidar da cewa dauki ba dadin ya wanzu ne a tsakanin magoya bayan kungiyyar Hamas da kuma na jam´iyyar Fatah, na gudana ne a gaza.

Rikicin wanda ke da nasaba da kokarin samun madafin iko na yankin, ya gudana ne a kusa da gidan shugaban yankin wato Mahmud Abbas.

Ko da a jiya lahadi, sai da wasu tsagerun yankin suka harba rokoki izuwa ofishin shugaban yankin na Palasdinawa, wanda hakan yayi ajalin mutane uku tare da jikkata wasu da daman gaske.

Ya zuwa yanzu dai faraministan yankin Ismail Haniyya, ya soki lamirin shugaba Mahmud Abbas da haifar da wannan rikici, ta bukatar daya gabatar na gudanar da zabe, a watan Afrilun sabuwar shekara. Zaben wanda aka shirya gudanarwa kafin lokacin da aka tsara, Mr Haniyya yace kungiyyar su ta Hamas zata kaurace masa.