Bangaren gwamnatin Siriya zai je Geneva | Labarai | DW | 28.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bangaren gwamnatin Siriya zai je Geneva

A na dai ganin da kamar wuya tattaunawar ta Geneva a samu nasara ganin yadda Shugaba Assad ke kara nasara a yakin da yake da masu adawa.

Tawagar jami'ai daga gwamnatin kasar Siriya za su isa birnin Geneva a ranar Laraba kwana guda sabanin yadda aka tsammaci zuwansu don tattaunawar zaman lafiya a wannan mako kan makomar Siriya. Kamfanin dillancin labarai na SANA ya bayyana haka. Tawagar jami'an gwamnatin dai sun ki zuwa a fara taron da su a wannan rana ta Talata saboda yadda 'yan adawa ke kara kira na cewa Shugaba Assad ya sauka daga kujerar mulkinsa.

Jakada na musamman daga Majalisar Dinkin Duniya da ke shiga tsakani kan rikicin na Siriya Staffan de Mistura ya bayyana da ma cewa ya samu tabbaci daga bangaren gwamnatin ta Siriya za su halarci zaman taron kamar yadda mai magana da yawun MDD Alessandra Vellucci ta fada wa manema labarai a birnin na Geneva.

A na dai ganin da kamar wuya tattaunawar a samu nasara ganin yadda Shugaba Assad ke kara nasara a yakin da yake da masu adawa da gwamnatinsa yayin da daga bangaren na 'yan adawa ke sake jaddada bukata ta ganin ya sauka daga mulkin kasar.