Bana babu zabe a Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 24.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bana babu zabe a Sudan ta Kudu

Majalisar dokokin Sudan ta Kudu ce ta kada kuri'ar kara wa'adin Salva Kiir ta yadda ba sai an yi zabe ba, sakamakon rikice-rikice.

Majalisar dokokin Sudan ta Kudu ta kada kuri'ar da ta amince da kara wa'adin jagorancin shugaba Salva Kiir da shekaru uku, abin da ya soke duk wani shiri na yin zabe a cikin wannan shekarar kamar yadda aka zata tun farko, a kasar da ta shafe watanni tana fama da rikici.

Wannan mataki dai, masu nazarin lamuran kasar sun ce zai kawo tangarda ga yunkurin masu shiga tsakani a yankin, wadanda suke kokarin gani shugaba Kiir da jagoran 'yan tawaye Reik Machar sun kafa gwamnatin hadaka wadda za ta kasance a matakin rikon kwarya, kafin zabe.

Yanzu dai 'yan tawayen sun fara kiran Kiir shugaban mulkin kama karya duk da hujjar da magoya bayansa suka bayar, na cewa an yi hakan ne dan gudun barin gibi a madafun iko, bayan da tattaunawar sulhun ta rushe, amma tabbas zai cigaba da neman hanyoyin sulhu.

Dama dai ranartara ga watan Yuli mai zuwa ne aka sa ran yin zabe a kasar da ke fama da rarrabuwar kawuna