Ban Ki Moon yi kira a kawo karshen yaki a Siriya | NRS-Import | DW | 25.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Ban Ki Moon yi kira a kawo karshen yaki a Siriya

Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya na tattauna shawo kan rikicin Siriya.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya nanata kira ga shugabannin manyan kasashen duniya su kara himma wajen kawo karshen ta'asar da ke faruwa a Siriya.

Ban Ki Moon ya baiyana hakan ne yayin wani taron kwamitin sulhun Majalisar Duniyar domin tattaunawa kan yadda yakin Siriyar ke kara yin kiamari.

Tun da farko manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniyar a Siriya Staffan de Mistura ya jaddada kira ga kwamitin sulhun ya tsara wani ingantaccen shiri don kawo karshen tashe tashen hankula a Siriya.

" Yace roko na ga kwamitin sulhu a yau shine a yi wa Allah a tsara manufa ta bai daya da za ta tilasta tsagaita wuta a Siriya. Na yi amannar cewa za mu iya sauya fasalin al'amura.

Mutane akalla 26 ne suka mutu a wani sabon luguden wuta ta sama da sojojin gwamnati suka yi a birnin Aleppo a cewar kungiyar kare hakkin bil Adama a Siriya wadda ke da mazauninta a Birtaniya.