1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ban Ki-Moon ya yi kira ga bengarorin Burundi

Salissou BoukariAugust 28, 2015

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon, ya yi kira a wannan Jumma'a ga bangarorinn kasar Burundi da su koma teburin tattaunawa domin samun mafita a rikicin kasar.

https://p.dw.com/p/1GNd9
Ban Ki-moon
Ban Ki-moonHoto: Reuters/T. Negeri

Wannan kira na zuwa ne kwanaki kalilan bayan kafa sabuwar gwamnati wadda ta kunshi mafi yawan magoya bayan shugaba Pierre Nkurunziza. A cikin wata sanarwa, da ke tunatar da zagayowar cika shekaru 15 da yarjejeniyar birnin Arusha wadda ta kawo karshen yakin basasan kasar, Ban Ki-moon ya ce babu lokacin da aka fi taka dokokin wannan yarjejeniya kamar 'yan watannin nan biyar na baya-bayan nan, inda ya yi kira ga 'yan kasar ta Burundi da su bai wa tattaunawa dama don samun sulhu a tsakani don kauce wa komawa ga yanayi na tashin hankali mai muni a wannan kasa. A ranar Talata ce dai shugaban kasar ta Burundi, ya nada sabin membobin gwamnati, inda masana ke ganin cewa shugaban na ci gaba da rike lamarin ba tare da buda wata kafa ta samun tattaunawa ba.