Ban Ki-Moon ya kai ziyara a kasar Somaliya | Labarai | DW | 30.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ban Ki-Moon ya kai ziyara a kasar Somaliya

Sakatare Janar na MDD ya kai ziyarar aiki zuwa Mogadishu babban birnin kasar Somaliya, tare da rakiyar shugaban Bankin Duniya cikin tsauraran matakan tsaro.

Ban Ki-Moon ya kai wannan ziyara ce, tare da Shugaban Bankin Duniya Jim Yong Kim, inda suka gana da Shugaban kasar Sheikh Mohamud a filin saukan jiragen sama da ke karkashin kulawar dakarun kiyaye zaman lafiya na Tarayar Afirka da ke samun tallafin Majalisar Dinkin Duniya. Fadar shugaban kasar ta Somaliya ta ce ganawar tana da nasaba ne da kara inganta lamura a wannan kasa da yaki na tsawon shekaru ya wargaza. Dakarun kiyaye zaman lafiya sun samu nasarar kwace mafi yawan wuraren da ke hannun tsagerun kungiyar Al-Shabaab masu kaifin kishin Islama.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu