Ban Ki-moon ya bukaci karin soje a Bangui | Labarai | DW | 21.02.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ban Ki-moon ya bukaci karin soje a Bangui

Majalisar Dinkin Duniya na kokarin aika karin dakaru dubu uku zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya domin kare fararan hulla daga cin zarafin da suke fuskanta.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon, ya bukaci Kwamitin Sulhu na Majalisar ya tura karin dakaru a kalla dubu uku da zasu hada da sojoji da 'yan sanda ya zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya cikin gaggawa domin sanya tsari tare da kariyar fararan hula a wannan kasa.

Ban Ki-moon ya kara da cewa wadannan dakaru za su isa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar ba da jimawa ba, kuma tare da isassun kayan aiki musamman ma jiragyen zirga-zirga a cikin wannan kasa mai Fadin gaske.

A halin yanzu dai, dakarun kasar Faransa dubu biyu, da na kasashen Afirka dubu shida, sannan da na Tarayyar Turai a kalla dari biyar ke wannan kasa. Amma duk da haka ana ganin karin dakarun na Majalissar Dinkin Duniya, wani babban abun da ake jira ne.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe