SiyasaJamus
Myanmar : An hana lauyan Suu Kyi magana
October 15, 2021Talla
Cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin mulkin sojan ta ce ta hana Khin Maung Zaw magana ne kasancewar kalamansa ka iya tayar da zaune tsaye a kasar. A wata ganawar karshe da 'yan jarida, lauyan ya gabatar musu da shaidar wani tsohon shugaban kasar da ya nada a gaban kotu, yana cewa sojojin da suka je kamashi da ya gwammace mutuwa maimakon ya yi marabus.
Tun bayan hambarar da ita daga kan karagar mulki sojoji a Myanmar ke zargin Aung San Suu Kyi da aikata manyan laifuka ciki har da na cin hanci, lamarin da ya janyo bore da ya yi sanadiyar mutuwar mutane dubu da 200 ba ya ga wasu fiye da dubu bakwai da ke hannun hukuma.