Bama-bamai sun tashi a arewacin Kamaru | Labarai | DW | 13.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bama-bamai sun tashi a arewacin Kamaru

Bama-baman guda hudu sun tashi ne a yankin Bamenda, na farko da misalin karfe tara na dare sauran uku kuma da misalin karfe uku na safiya.

Wasu bama-bamai sun tashi a yankin Kamaru da ke magana da harshen Ingilishi, sai dai rahotanni daga jami'an gwamnati sun nunar da cewa babu wanda abin ya shafa. Bama-baman guda hudu sun tashi ne a yankin Bamenda na farko da misalin karfe tara na dare sauran uku kuma da misalin karfe uku na safiya kamar yadda jami'an tsaro bayan tuntubar mahukunta a yankin Yaounde suka bayyana, sun kuma kara da cewa babu wanda abin ya shafa. Sai dai wani jami'in tsaro a birnin na Yaounde ya ce akwai wadanda abin ya shafa sai dai abin bai kazanta ba.