1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane hudu sun jikkata

January 7, 2021

Wani bam ya tarwatse kuma ya hallaka sojoji hudu da farar hula guda a arewacin Kamaru.

https://p.dw.com/p/3ncQV
Kamerun Selbstmordattentat in Kolofate
Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

Wani abu mai fashewa ya tarwatse tare da hallaka sojojin Jamhuriyar Kamaru guda hudu da kuma wani farar hula guda, a yankin Ambazoniya na masu amfani da turancin Ingilishi.

Kimanin mutane uku ne aka samu rahoton cewa sun jikkata, wadanda kuma yanzu haka suna karbar magani a wani asibiti.

Mai magana da yawun rundunar sojin kasar Rene Emmanuel Sadi ya bayyana cewa abin ya rutsa da dakarun nasu ne, yayin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga wurin wani biki a yankin Mbengwi.

Wasu alkalumma sun bayyana cewa akalla sama mutane dubu uku ne suka rasa rayukansu, inda kuma wasu sama da dubu dari bakwai suka tsallake matsugunnansu tun bayan zafafa hare-haren da 'yan tawayen suka yi a shekara ta 2017.