Bam ya halaka mutane kimanin 60 a Pakistan | Labarai | DW | 25.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bam ya halaka mutane kimanin 60 a Pakistan

Hukumomin 'yan sanda a kasar, sun tabbatar da mutuwar mutane a wani mumunar harin kunar bakin wake da 'yan bindiga suka kai a makarantar horasda 'yan sanda da ke kudu maso yammacin birnin Quetta.

Jami'an 'yan sanda sun ce maharan rufe da fuskokin su dauke da manyan makamai suka kusa cikin makarantar, tare da bude wuta na kan mai uwa dawabi daga bisani wasu mutum uku suka tashi jigidar bama-bamai da ke jikin su. Wannan harin ya yi sanadiyar jikkata mutane sama da 117, sannan 'yan bindigan sun yi garkuwa da wasu 'yan sanda. Jam'ian tsaron soji da ke kusa da makarantar sun bindige daya daga cikin maharan da ke kokarin tashin bam da ke jikinsa.  

Akwai sama da 'yan sanda 700 da ke samun horo a makarantar a lokacin da aka kai harin, amma kawo yanzu babu wata kungiya da ta dau alhakkin wannan hari dama dalilan kai mumunar harin a makarantar horasda 'yan sanda. Amma hukumomin tsaro a kasar na cewa wannan hari shine mafi muni da ya hallaka mutane da dama kuma ana alakanta harin da mayakan Sunni na Lashkar-e-Jhangvi.