Abdulkadir Balarabe Musa ya zama gwamnan mulkin farar hula na farko a Jihar Kaduna lokacin Jamhuriya ta biyu a shekarar 1979.
An zabeshi karkashin jam'iyyar PRP. Ya kuma zama gwamna na farko da aka tsige a majalisar dokoki a shekarar 1981 sakamakaon sabani da 'yan majalisa na bangaren jam'iyyar NPN mai mulkin Najeriya a lokacin. Har yanzu ana girmama shi a fagen siyasar kasar.