Bakin hauren Afirka sun samu matsala a teku | Labarai | DW | 16.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bakin hauren Afirka sun samu matsala a teku

Jiragen ruwa shida dauke da bakin haure da dama sun makale a tsakiyar teku. Sai dai masu tsaron ruwan Italiya na kokarin cetosu bayan da suka nemi agaji.

Jami'an Italiya da ke sa ido a kan mashigin ruwan kasar sun bayyana cewa sun kaddamar da wani yunkuri na ceto wasu bakin haure na kasashen Afirka da suke tangal-tangal a tsakiyar teku. Su dai masu sun shigowa Turai ta ko halin kaka ne suka nemi agaji bayan da jiragen ruwan da aka makarasu suka ci karo da matsaloli bayan da suka taso daga kasar Libiya. Jiragen ruwan shida ne ake kokarin cetowa yanzu haka.

Wannan dai shi ne karo na biyu da hukumomin na Italiya ke kokarin ceto rayukan bakin haure da ke hadari a cikin teku baya ga wanda ya wakana a ranar Jumma'a da ta gabata. Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa fiye da mutane dubu uku da ke neman mafaka a kasashen Turai ne suka rasa rayukansu a ruwan na Italiya a shekarar da ta gabata.