Bakin haure sun ci karfin ′yan sadan Macedoniya | Labarai | DW | 22.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bakin haure sun ci karfin 'yan sadan Macedoniya

Daruruwan bakin haure suka tsallaka zuwa kudancin kasar bayan da suka yi nasarar ketara shingen wayar bayan fin karfi da suka yi wa tarin jami'an tsaro da kasar ta jibge

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP wanda shi ne ya ruwaito labarin, ya ce bakin hauren wadanda akasarinsu 'yan asalin kasar Siriya ne, sun yi ta lankwasa shingen wayar suna tsallakawa, duk da jerin gurneti da hayaki mai sa kwalla da harbin sama wanda 'yan sandan suka yi ta jefawa domin tsorita bakin hauren.

Bakin hauren sama da dubu biyu ne dai suka ja daga tun ranar Alhamis din da ta gabata a kan iyakar kasar ta Macedoniya da kasar Girka. Lamarin ya faru ne a iyakar kauyen Idomeni na kasar Girka da kuma birnin Gevgelija na kasar ta Macedoniya. Yan gudun hijira sama da dubu da 500 ne a cewar kamfanin dillancin labaran na AFP, suka yi nasara tsallakawa kafin 'yan sandan su yi nasarar sake gicce shigen.