Bakin haure 35 sun halaka a tekun Libiya | Labarai | DW | 08.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bakin haure 35 sun halaka a tekun Libiya

An dai samu dama ta ceto bakin haure 85 ciki kuwa har da mata 18 bisa tallafi na masunta wadanda suka ankarar da jami'an da ke lura da gabar teku.

Bakin haure 35 ne ciki har da kananan yara bakwai suka bace sakamakon nutsewar jirginsu a teku bayan sun baro gabar teku a Libiya. An dai samu dama ta ceto wasu daga cikin bakin hauren kamar yadda jami'an da ke lura da gabar teku suka bayyana.

An samu dama ceto bakin hare 85 wadanda suka hada da mata 18 bisa tallafi na masunta wadanda suka ankarar da jami'an da ke lura da gabar tekun kamar yadda Issa al-Zarrouk, jami'i da ke aiki a cikin jami'an da ke lura da yankin Garabulli mai kimanin tazarar kilomita 60 daga Gabashin Tripoli.