Babu sauran Ebola a Yammacin Afirka | Labarai | DW | 09.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Babu sauran Ebola a Yammacin Afirka

Bayan shekarun da aka yi ana fama da annobar Ebola yanzu dai Kungiyar Lafiya ta Duniya wato WHO ta tabbatar nasasarar kauda cutar baki daya

Kungiyar Lafiya ta Duniya wato WHO, a yau Alhamis ta fidda sanawar tabbacin kawar da annobar cutar Ebola a Yammacin Afirka. Wannan ya biyo bayan da WHO ta wanke kasar Laberiya daga annobar. Kwanaki shida da suka gabata ma, kungiyar ta wanke kasar Gini, inda cutar ta samo asali a shekaru uku da suka gabata. Tun tsakiyan watan Maris da ta gabata, WHO ta ayyana kauda cutar a kasar Saliyo, wacce ke zama kasa ta uku da annobar Ebola ta shafa. Dama dai kasashen Gini, Laberiya da Saliyo sune kasashen Yammacin Afirka uku da annobar cutar Ebolan ta yi kamari a cikinsu. Cutar da ta yi sanadin mutuwar kimanin mutane dubu 110,000.