Babu gasar kwallon Afirka a 2015 a Moroko | Labarai | DW | 09.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Babu gasar kwallon Afirka a 2015 a Moroko

Bisa dalilan fargabar yaduwar cutar Ebola, hukumomin Moroko sun ki daukar nauyin shirya gasar kwallon kafa ta kasashen Afirka ta shekara mai zuwa.

Kasar Moroko ta tabbatar da cewa ba za ta dauki bakwancin gasar cin kofin kwallon kafa ta kasashen Afirka a watan Janairu na shekara mai zuwa ba bisa dalilai na kiwon lafiya. Cikin wata sanarwa da ma'aikatar wasannin kasar ta fitar, ta ce ta na fargabar yaduwar cutar Ebola tsakanin al'umma sakamakon barazana da ta ke yi ga rayukan jama'a.

Kusoshin kwallan kafar Moroko sun dauki wannan matakin ne saboda fatali da bukatarsu da Hukumar Kwallon kafa ta kasashen Afirka ta yi na kin dage gasar har i zuwa shekara ta 2016. Ita dai Moroko za ta iya fuskantar fushin CAF, wacce za ta iya dakatar da ita daga gasannin da za ta shirya nan gaba.

Hukumar Kwallon kafar ta kasashen Afirka za ta gudanar da taro a ranar Laraba mai zuwa domin nazarin kasar da za ta dauki bakwancin gasar. Idan dai za a iya tunawa tarayyar Najeriya ta nuna sha'awar daukar bakwancin gasar kwallon ta badi.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Pinadi Abdu Waba