Babu ci gaba a game da rikicin Darfur | Siyasa | DW | 28.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Babu ci gaba a game da rikicin Darfur

Har yau ana fama da lalube a cikin dufu wajen shawo kan rikicin Darfur

'Yan gudun hijirar Darfur

'Yan gudun hijirar Darfur

Tun abin da ya kama daga shekara ta 2003 ne ake fama da yaki a lardun Darfur na yammacin Sudan. Kuma kawo yanzu sama da mutane dubu metan suka yi asarar rayukansu a yayinda wasu miliyan uku ke kan gudun hijira sakamakon wannan yaki da Larabawa ‘yan janjaweed suka gabatar kan bakar fatar lardin tare da goyan bayan gwamnati a fadar mulki ta Khartoum. Da yawa daga manazarta na kwatanta ta’asar dake faruwa a Sudan da wadda ta wakana a kasar Ruwanda a cikin shekarun 1990, illa kawai ita ta Sudan ana yinta ne sannu a hankali. Jami’an MDD ma batu suke a game da wani yunkuri na yi wa kabilun bakar fata ‘yan usulin lardin Darfur kisan kare dangi. Shi kansa wakilin majalisar akan al’amuran Sudan Jan Pronk sai da ya fito fili ya bayyana takaicinsa a game da gazawar da kafofi na kasa da kasa suka yi wajen samar da zaman lafiya a lardin na Darfur. Domin tinkarar wannan gazawa shugaba Goerge W. Bush na Amurka yayi kiran tura karin sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD da zasu rufa wa sojan kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afurka baya, lamarin da ‘yan tawayen Sudan suka yi marhabin da shi kamar yadda aka ji daga bakin Brahim Ahmad Ibrahim, kakakin kungiyar SPLA dake da hannu a gwamnatin hadin gambiza ta kasar Sudan a halin yanzu haka.

“Ina ba da cikakken goyan baya ga shawarar ta shugaba Bush. Wajibi ne a turo wannan runduna a cikin gaggawa. Domin kuwa a kowace rana ta Allah sai an yi asarar rayukan mutane masu tarin yawa sakamakon hare-haren da ake famar kaiwa kan sansanonin ‘yan gudun hijira. Al’umar Darfur na bukatar kariya daga sojojin MDD.”

Amma fa ita gwamnatin Sudan ta fito fili ta bayyana adawarta da shawarar tura sojojin na MDD tana mai cewar bata so a yi mata shisshigi a al’amuranta na cikin gida. Su kuma a nasu bangaren kasashen Rasha da China sun kiya faufau a game da kakaba wa fadar mulki ta Khartoum matakai na takunkumi a zaman taron da kwamitin sulhu na MDD yayi a jiya litinin a bayan fage. A dai farkon watan fabarairun nan ne kwamitin sulhu ya bayyana shirinsa na tura rundunar kiyaye zaman lafiyar da zata jagoranci matakan neman zaman lafiyar lardin Darfur da kuma rufa wa sojan kiyaye zaman lafiya na kasashen Afurka baya. Ita ma Jamus ta bayyana goyan bayanta ga wannan mataki, kuma gwamnati na fatan ganin an ci gaba da matsin lamba akan dukkan bangarorin dake da hannu a wannan rikici in ji Gernot Erler, karamin minista a ma’aikatar harkokin wajen Jamus, wanda ya kara da cewar:

“Matsin lambar zata fi tasiri ne idan aka samu hadin kai tsakanin KTT da MDD. Kuma wajibi ne a kakaba wa daidaikun jami’an da lamarin ya shafa takunkumi, kamar dora hannu kan kudadensu na ajiya a bankuna da haramta musu tafiye-tafiye, musamman ma dangane da wadanda aka same su da alhakin keta haddin dan-Adam kai tsaye.”