Ba'asin zargin Facebook da cutar da yara | Labarai | DW | 05.10.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ba'asin zargin Facebook da cutar da yara

'Yan majalisar Amurka sun zargi shugaban kamfanin Facebook Mark Zuckerberg da mayar da hankali kan yin riba, ba tare da la'akari da bada kariya ga masu amfani da shafin ba.

'Yan majalisar Amurka sun bukaci da a gudanar da bincike kan zargin da mai kwarmata bayanan kamfanin ta yi na cewar, shafin sada zumuntar na cutar da yara kanana da haifar da rarrabuwar kawuna.

Ba'asin na mai tonan asiri Frances Haugen a gaban majalisar dottijan Amurkan na zuwa ne yini guda, bayan matsalar daukewar da shafin sada zumunta na Facebook da dangoginta na Instagram da WhatsApp suka yi na tsawon sao'i shida.

Shugaban karamin kwamitin harkokin kasuwanci Senata Richard Blumenthal na jam'iyyar Demokrat ya ce, Facebook na sane da cewar ya kan jarabci masu ma'amala da shi kamar sigari, "kuma 'ya'yanmu ne ke cutuwa" don haka wajibi ne Mark Zuckerberg ya bayyana don bada ba'asi a gaban kwamitin.