Ba ′yan ta′adda ne kawai ke cin zarafin jama′a | Siyasa | DW | 25.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ba 'yan ta'adda ne kawai ke cin zarafin jama'a

Kungiyar kare hakkin jama'a ta Amnesty International ta fidda rahoton ta na bana, inda kungiyar ta ce bayaga 'yan ta'adda, suma jami'an tsaron gwamnati na aikata laifin a fagagen daga.

Batun kungiyoyin 'yan ta'adda kama da ga Boko Haram a Najeriya, izuwa kungiyar IS a Siriya da Iraki dama Kungiyar Al-Shabab dake kasar Somaliya, gami da bullar tashin hankalin addini a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Wannan sune suka fi rinjayar rahoton na bana da kungiyar mai kare hakkin jama'a ta fitar kan al'amuran da suka wakkana a bara. Sai dai rahoton ba wai ga kungiyoyin 'yan ta'adda ya soka ba, amma har su kansu jami'an tsaro a wasu kasashen. Inda Steve Crawshaw darakta a kungiyar ta Aminesty International, ya bada misali da Najeriya.

"A Najeriya misali, an mayar da hankali matuka kan mummunan aikin da BHaram ke yi wa jama'a, amma kuma akwai wasu laifuka dama da suka gano wanda sojojin Najeriya ke aikatawa kan farenhula. Inda sojojin aka samu shaidun yadda suke fille kawunan mutanen da suka kama suna zarginsu da kasancewa 'yan Boko Haram. Akwai fayafayen bidiyo da ke bada hujjar hakan. To amma dai aikata wannan aikin dabbanci, a bagaren kungiyoyin mayaga daga sassa daban-daban na duniya, a bara ya yi kamari fiye da ko wane lokaci"

Wata babbar matsala bayaga 'yan ta'adda irinsu Boko Haram da sauran kungiyoyin 'yan ta'adda, a kasashen masu tasowa kamar na Afirka, Amnesty ta ce akwai muzgunawa yancin walwala da fadin albarkacin bakin jama'a da gwamnatoci ke yi. Kamar yadda Netsanet Belay darakta mai kula da binciken al'amuran Afirka a kungiyar ta Amnesty International.

"Wasu kasacen sun hada da wadanda aka sansu dama can da danne yancin al'ummarsu, kamar kasashen Habasha, Burundi da Eriteriya. Mun kuma shadai yadda wasu kasashen ke yin dokoki da sunan yaki da ta'addanci, inda ake labewa da hakan ana cin zarafin 'yan jarida da masu fafitika. Kana akwai batun muzgunawa masu zanga-zanga, kamar a kasashen Angola, Burundi, da Gambiya. Don haka akasarin kasashen Afirka munga hukumomi na ci gaba da gallazawa jama'a"

To sai dai fa a cewar kungiyar ta Amnesty International ba ta ko wane bangare ake samun koma baya ba, misali bangaren kare tsiraren jinsi na ingantuwa, a cewar daraktan mai nazarin al'amuran Afirka.

"Eh lallai ta bangaren za mu iya cewa bara, shekara ce da aka samu nasara. Babban nasarar ita ce, kudurin da hukumar kula da hakkin jama'a da kungiyar AU ta yi. inda suka amince da kudurin kare yancin dukkan dan Adam, ba tare da yin la'akari da jinsa mace ce ko na miji ba. Wannan babban abun a yaba ne muka samu, daga kungiyar kare yancin jama'a na nahiyar Afirka. Mun kuma ga ci-gaba a kotunan wasu kasashen, misali a kasar Yuganda inda kotu ta soke dokar haramta auren jinsi daya. Hakama a kasar Botswana kotu ta soke irin wannan doka da ke nuna wariya ga masu luwadi ko madigo. Wadannan sune 'yan kadan daga kekkewar fata da muka gani a bara."

Sai dai duk wadannan nasarori, kungiyar Amnesty International, ta ce batun tauye yancin jama'a abune da ke da tarin yawa, don haka suke ci-gaba da fafitikar ganin hukumomi da lamarin ya rataya a kansu, suna kare hakkin al'ummar da suke mulka.

Sauti da bidiyo akan labarin