B Haram: Yiwuwar sakin ′yan matan Chibok bisa sharadi | Siyasa | DW | 09.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

B Haram: Yiwuwar sakin 'yan matan Chibok bisa sharadi

Wani kamfanin dillancin labaran kasar Amirka ya ruwaito cewar kungiyar ta Boko Haram ta yi tayin sakin 'yan matan na Chibok a madadin kwamandojinta da ke tsare.

Kasa da awoyi 24 da ganawar farko a tsakanin masu fafutukar ceto 'yan mata yan makaranta na Chibok da kuma shugaban tarayyar Najeriya, alamun haske ya fara tare da kungiyar bada tayi na sakin 'yan matan da nufin musaya da wasu kwamandojin kungiyar 16.

Wani kamfanin dillancin labaran kasar Amurka dai ya ruwaito sabon tayin da ke zaman irinsa na farko a bangare kungiyar da ke shan zafi yanzu. Kamfanin AP dai ya ce wani mai fafutukar da bai so a ambaci sunansa ba, na cikin tsakiyar tayin da ya tanadi sakin daukacin 'yan matan 219 a madadin kwamndojin da ke warwatse gidajen yarin kasar daban daban.

To sai dai kuma babu sahihanci na lokaci dama wuri na fara shirin sulhunta tsakanin ga kungiyar da shugabanta ya bace daga labarai tun bayan tabbatar da sabuwar gwamnati a kasar.

Ya zuwa yanzu dai akwai alamun sauyin ragamar yakin da ke kallon kwace daukacin sansanoni da ke hannu na kungiyar a can baya, sannan kuma da takaita aiyyukanta zuwa kuna ta bakin wake jifa jifa.

Abun kuma da ke iya tilasta musu neman sulhuntawar da kila ma yarda kwallon mangoro domin hutawa da kuda.

An dai ruwaito wani jami'in diplomasiyar Birtaniya da ke nan a Abuja na fadin sun gano inda 'yan matan ke tsare sai dai akwai hatsari a kokarin cetonsu da karfi na hatsi a hannun kungiyar da ke musu kallon jarin karshe ga makoma.

To sai dai kuma akwai tsoron yiwuwar amfani da sabon tayin da nufin damfara ga gwamnatin da a baya ta sha rabuwa da kudade mai tsoka a hannun masu ikirarin nemo mafita.

Abun kuma da a fadar Dr. Jibrin Ibrahim da ke zaman bin diddigin yakin kasar ta Najeriya da ma kokarin ceto 'yan matan, ya sanya taka tsantsan zama na wajibi a kokarin tantance gaskiyar ikirarin da bashi da suna balle tsari.

Sauti da bidiyo akan labarin