Azumin watan Ramadana a sassan duniya daban-daban
July 18, 2013Talla
Musulmai a nan tarayyar Jamus sun bi sahun takwarorinsu na kasashen duniya wajen gudanar da wannan aiki na ibada. Sai dai a bana kasancewa watan na Ramadana ya zo ne a lokacin bazara a kasashen Turai da kuma arewacin Amirka inda tsawon rana kan kai kimanin awowi 19 ga kuma tsananin zafi, ya sa wasu Musulman dake aikin karfi, sun ajiye azumin har sai lokacin da yanayi ya canja.