Tsadar kayan marmari cikin watan Ramadana a Nijar | Zamantakewa | DW | 18.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Tsadar kayan marmari cikin watan Ramadana a Nijar

Da ƙaratowar azumin watan Ramadana mai alfarma, farashin kayayyakin masarufi sun yi tashin gwauron zabi abin da ya sanya al'umma kukan samun rangwame.

A yayin da a ƙasashe daban-daban na duniya al'umma musulmi suka maida hankalinsu ga shiriye-shiriyen kama azumin watan Ramadana, a jamhuriyar Nijar ƙasar da musulunci ya kwashe kimanin kashi casa'in da 'yan kai cikin ɗari, magidanta sun fara bayyana fargabarsu game da tsadar farashin kayan masarufi wanda suke a matakin farko daga cikin kayan da magidanta ke tanadi kafin tsayuwar watan.

Haƙiƙa biri ya so ya yi kama da mutum game da hawan farashin kayan masarufin da ya afku, ta la'akari da sakamakon alƙaluman hukumar INS a kan farashin abincin da ta wallafa na farkon watan Yunin da ya gabata, inda farashin Gero, Masara da Dawar gona suka ƙaru, saɓanin shekarar bara inda a wannan lokaci ana daf da kama azumi farashin ya faɗi kasa warwas.

To ko yaya magidanta ke ciki game da batun shiriye shiriyen kama Azumin na bana? ga su Ibbo Leko da karin bayani.

"Muna so in watan azumi ya kama a sassauta farashi kowa ya ji dadi."

Shi kuwa Malam Illa Sunana magidancin cewa ya yi "Sai ka yini ba ka samu abun da ya shafi dallar Amirka ɗaya ba, wannan shi ne babbar matsalar, shugaban ƙasa ya taimaka a karya farashin kayan abinci a yi irin na lokacin shekarun baya shinkafar jaka 24 a kawo mana yadda zamu same ta sha wani abu".

"Ni Rabi sunana komai ya yi tsada fisabillilahi gwamnati ta duba ta gani ta yi wa al'ummar musulmi farashi mai kyau, wani abin da za ka ji maiƙo dole ne sai ka saya 'yan kasuwa in sun sayo abun da ragi sai su sanya riba mai yawa"

Ƙalubalen da ke tattare da tashin farashin kayayyakin

Wani babban ƙalubale da ya sa jama'a cikin fargaban hawan farashin kayan masarufin shi ne yadda ƙananan 'yan kasuwa ke bayyana cewar tsayuwar watan azumin suke jira ko za su dace da cinikin kayan buɗe baki kamar yadda su Malama Balki mata masu kayan ɗanye suka tabbatar ma DW.

"Kamar kashin mu na na goma mu na na ƙadago mu na tafasa mu na zogala in aka kama azumi idan azumi ya zo ku kan ɗan sauke farashin ku? farashin ƙarashi ma muke yi, ana so in aka sha ruwa a ɗan kwada a ɗan buda baki"

"Sunana Zuway cinikin Zogala Alhamdullilahi ana kankamawa kuma in azumi ya kama tafi haka ɗanya ce muke saidawa mu ba ma saida busassa saboda ɗanyar tafi kasuwa."

Wannan hawan farashi dai ba a Gero ko Masara da Dawar gona, da kayan buɗa bakin ya tsaya kadai ba, har ma da kayan haɗa sanfa dake zaman maraka ko ma iyayan tafiya wani ɗan kasuwar irin waɗannan kaya mai sunan Laminu ya bayyana irin ta sa hajar da yake sayarwa

Sauran kayayyakin da tashin farashin ya shafa

"Muna saida kamar gujiyar miya, yajin yawo da garin da kuri da sauransu dai wanda muke ɗan harhaɗawa a cikin kayan miya ɓangaren kayan tukudi kuma akwai garanfani akwai hakin daka akwai kelawai akwai hakin zango to a yanzu halin da muke ciki ma gaba daya duk kayayyakin sun samu ƙarin kudi, kaya ya shigo da tsada haka ɗan kasuwa da wannan yanayin zai saida shi."

To ko me ke kawo wannan matsalar hawan farashin kayan abinci a daidai lokacin da ake tinkarar azumin watan Ramadana wanda kuma jama'a ke ɗora laifi ga 'yan kasuwa? ita ce tambayar da na miƙa ga wani ɗan kasuwa, Abdulƙadir Malam Sani.

"Matsalar farashin kaya da ake wani karon, mutanen suke janyo abun da bakinsu, kayan tun bai kai ba ake cewa in azumi ya zo kaza zata yi tsada, komi ma zai yi tsada."

Tuni dai a farko-farkon watan Sha'aban ne malaman addinin musulumci suka maida hankalinsu ga kiraye-kiraye zuwa ga 'yan kasuwa da masu hannu da shuni da su nisanci doguwar riba don taimaka wa masu ƙaramin ƙarfi ko sun dace da albarkatun dake tattare da wannan wata na Ramadana.

Mawallafi: Larwana Malam Hami
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin