Azumin Ramadan a yanayin annobar Corona | Labarai | DW | 13.04.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Azumin Ramadan a yanayin annobar Corona

Musulmi a fadin duniya sun fara azumi watan Ramadan na shekarar 2021 a daidai lokacin da ake cigaba da fama da annobar Corona.

A kasashe irin su Indonusiya an kama azumin ne cikin tsauraran dokokin yaki da annobar Covid-19 sai dai mahukuntan kasar sun bayar da damar bude masallatai albarkacin wannan wata mai tsarki tare da daukar matakan kariya na amfani da kyalen rufe baki da hanci da kuma bada tazara a tsakanin jama'a musamman wajen sallar Tarawih.

A kasashe matalauta, matsin tattalin arziki ne ke kan gaba wajen takura masu azumin.