1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aza ayoyin tambaya bisa bacewar 'yan matan Chibok

Usman ShehuMay 2, 2014

Sharhunan jarudun Jamus na wannan makon sun fi mayar da hankali ne bisa tashin hankali da ke faru a Tarayayar Najeriya, musamman sace yan matan Chibok .

https://p.dw.com/p/1Bt0t
Nigeria Protest
Hoto: DWU. Abubakar Idris

Bari mu fara da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, inda ta aza ayar tamba cewa, wai shin ina 'yan matan Chibok suka bace ne? Jaridar ta ci gaba da cewa, yau kusam makwanni uku da sace 'yan mata sama da 200 a jihar Borno, amma har yanzu babu duriyarsu. Acewar jaridar wannan matsalar an san cewa ta shafi kungiyar Boko Haram ne, amma kuma fa a zahiri akwai ma sarkakiya ta siyasa a Najeriya. Sukar da ake yi wa sojojin Najeriya bisa rashin kwato 'yan matan sai karuwa yake yi. Kai wata babbar matsala da nuna yadda lamarin tsaro da kare lafiyar bil'Adama ya fito a fili, shine, ko da yawan alkaluman 'yan matan da aka sace akwai maganganu da ke karo da juna. Misali gwamnan jihar ta Borno yace 'yan mata 129 aka sace, ita kuwa shugabar makaranatar Asabe Aliyu Kwarmbula, ta ce fa ita kam dalibanta 187 aka sace. Sai kuma daga baya jami'an tsaron Najeriya ke cewa ai wadanda aka sace sun kai sama da 270. Batun dai ya zama kamar wasan yara, inda da fari ma sojojin suka ce an kubatar da 'yan matan in banada 9. A yanzu dai abinda aka sani shi ne, 'yan mata kusan 40 sun kwato kansu daga hannun masatan, kuma akasari 'yan shekaru 12 izuwa 18 wadanda aka sacen.

Nigeria Protest
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Sai jaridar Süddeutscher Zeitung, wanda ta mayar da hankali bisa wani rikicin da yaki ci yaki cinyewa. Wato Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Jaridar ta ce yanzu kam sojojin MDD sunn fara isa bakin aiki. A makwan jiya wani harin da mayaka suka kai a asibiti da ke kasar, ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 22, ciki harda ma'aikatan agaji na kungiyar Doctors Without Borders. A Cewar jaridar tun farkon bana mayakan kungiyar Anti-Balaka ta Kiristoci ke ta zafafa hare-haren kan tsiraru musulmai, inda 'yan Anti-Balakan ke zargin cewa musulman sun goyi bayan Seleka, wanda ta kwace mulkin kasar a baya. Yanzu dai a kammala kwashe musulmai daga birnin Bangui, inda aka kaisu wasu biranen arewacin kasar da ake ganin za su fi samun tsira. A cewar jaridar kimanin musulmai 1200 sojojin MDD suka yi wa rakiya domin su fice daga birnin Bangui.

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung, ta maida hankali ne kan tsagaita wuta da ka cimma tsakanin gwamnatin Sinigal da 'yan tawayen kudancen kasar na yankin Casamance. Inda jaridar ta ci ga da cewa, fatan zaman lafiya a Casamance. Wannan dai ya biyo bayan sahannun kan tsagaita wuta wanda shugaban 'yan tawayen Salif Sadio ya ayyanar. A ranar Laraba da ta gabata ne dai, jagoran 'yan tawayen na kungiyar MFDC mai neman yantar da yankin Casamance ya fidda sanawar. A cewa wannan jaridar, matakin wani ci gabane kan turbar samanr da zaman lafiya, a wannan rikin da aka yi tsawon shekaru ana fama da shi. Dama tun bayan zaben shugaban kasar Sinigal Makcy Sall, babu wani daukar makami da aka samu tsakanin gwamnati da 'yan tawaye, sabanin zamanin tsohon shugaba Abdullahi Wade.

Senegal Senegalesische Soldaten
Hoto: AFP/Getty Images

A karon farko sojojin Jamus sun shiga aikin kiyaye zaman lafiyan a kasar Somaliya da ke gabashin Afirka. Wannan shi ne labarin jaridar Berliner Zeitung. Tura sojojin na Jamus a Somaliya dai na cikin tsarin kungiyar EU, wanda ke shirin horar da sojojin kasar Somaliya, kasar da ta yi fama da yakin basa, wanda kuma ya dai-daita dukan harkokin kasar. A yanzu sannun a hankali ana farfado da ma'aikatu, kana koda yake 'yan kungiyar Al-Shabab na kai farmaki jifa-jifa, amma dai an yi nasarar fatattakarsu daga manyan biranen kasar.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mohammed Nasiru Awal