1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ayyukan agaji a Bangladesh

Ibrahim SaniNovember 20, 2007
https://p.dw.com/p/CJUH

A can Bangladesh, Jami´an agaji na ci gaba da tallafawa waɗanda bala´in guguwar nan ta Sidr ta afkawa. Jami´an na amfani da ƙananan jiragene, wajen jigilar abinci da magunguna ga mutanen. Hakan kuwa ya biyo bayan yadda ruwan sama ya mamaye yankin da wannan annoba ta faɗawanne.Yankin kudu maso yammacin ƙasar dai a cewar rahotanni shi ya fi fuskantar ta´annatin Guguwar ta Sidr. A yanzu haka dai mutane sama da dubu uku Guguwar ta yi sanadiyyar rayukansu.Bugu da kari Guguwar ta kuma yi sanadiyyar jikkatar wasu Mutanen da daman gaske. A yanzu haka dai Jamus ta ruɓanya tallafin data bawa ƙasar ,daga Yuro dubu ɗari biyar izuwa Yuro miliyan ɗaya.