AU na neman zaman lafiyar Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 16.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

AU na neman zaman lafiyar Sudan ta Kudu

Ana dab da cimma yarjejeniyar zaman lafiya a Sudan ta Kudu bayan da AU ta yi yunkuri dinke baraka tsakanin masu yaki kan shugabanci da tsaro, abin da ya haddasa mutuwar dubban fararen hula tare da rabasu da matsugunansu.

A wanna Jumma'a ake sa ran kammala tattaunawar yarjejeniyar wanzar da zaman lafiyar kasar Sudan ta Kudu a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, wani wakilin MDD ya ce tattaunawar da aka fara shi makonni biyu da suka gabata, na cike da fatan samun matsaya da zai kawo karshen yakin basasar da kasar ke ciki na tsawon shekaru biyar.

Kungiyar Tarayyar Afirka AU da Kwamitin sulhu na MDD, sun yi gargadin sanya takunkumi kan wadanda ke wargaza yarjejeniyar da za a rattabawa hannu a ranar Asabar. Koda yake a baya kasar Amirka ta sanyawa Sudan takunkumin hana sayan makamai, abin da ya hargitsa 'yan kasar fita zanga-zangar nuna adawa.