Asusun IMF ya gargadi gwamnatoci kan kai jama′a makura | Labarai | DW | 30.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Asusun IMF ya gargadi gwamnatoci kan kai jama'a makura

Shugabar asusun bayar da lamuni na duniya wato IMF, Christine Lagarde ta gargadi gwamnatocin kasashen yankin arewacin Afirka da na Gabas ta Tsakiya kan inganta rayuwar al'ummarsu.

Lagarde ta ce kada a kai jama'a makura don kuwa sun kosa da yanayin rayuwar a cikin kasashen na su. Shugabar ta asusun IMF ta bukaci gwamnatocin da su gaggauta samar da shiri da zai biya wa al'umma bukatunsu.

Lagarde ta fadi hakan ne a yayin jawabinta a babban taro da ya hada kan wasu shugabannin kasashen duniya da ma masu hannu da shuni. Taron na kwanaki biyu na gudana ne a birnin Marrakesh na kasar Moroko. Taron ya mayar da hankali kan yakar matsalar cin hanci da rashawa da kuma kokarin inganta masana'antu da samar wa jama'a aikin yi,.

Wani rahoto na asusun lamunin ya nunar da cewa, kasashen yankin Gabas ta Tsakiya da na arewacin Afirka suna fama da matsalar nan ta karancin ma'aikata a sanadiyyar rashin bai wa mata damar yin aiki kamar sauran 'yan uwansu maza.