1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

IMF ya amince ya ba wa Burkina Faso karin tallafin kudi

February 19, 2026

Asusun Lamuni na duniya IMF zai gwangwaje Burkina Faso da karin tallafin kudi da ya kai kusan dala miliyan 34, bayan ya yaba da yadda mahukuntan kasar ke tafiyar da tsare-tsarensa.

https://p.dw.com/p/590vf
Russland Moskau 2025 | Treffen zwischen Wladimir Putin und Ibrahim Traoré zum 80. Jahrestag des Sieges
Hoto: Stanislav Krasilnikov/RIA Novosti/Anadolu/picture alliance

Asusun Lamuni na duniya IMF ya amince ya ba wa Burkina Faso dala miliyan 33,2 take yanke a matsayin zango na hudu na wani bangare na shirin ba da agaji ga kasar da ke yammacin Afirka.

Wannan sabon kaso na nuna cewa jimilla kudaden da Burkina Faso ta samu daga Asusun na IMF a matsayin agaji sun tashi a dala miliyan 165,8 kamar yadda sanarwar hukumar ta nunar.

A daura da wannan tallafi, Asusun IMF ya kuma sahale bai wa Burkina Faso rancen dala miliyan 124.3 da za ta biya a cikin dogon lokaci a karakashin wani shiri na yaki da dumamar yanayi mai lakabi da 'RSF'.

A watan Satumban 2023 ne dai Asusun IMF ya amince da wani shiri na ba wa Burkina Faso tallafin dala miliyan 305 domin karfafa wa hukumomin kasar gwiwa wajen yakar talauci a tsakanin al'umma.