Asusun IMF: An sake zabar Lagarde | Labarai | DW | 19.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Asusun IMF: An sake zabar Lagarde

Kwamitin gudanarwar asusun bisa jagorancin Aleksei Mozhin, ya bayyana Mis Christine Lagarde a matsayin mace hazika da ta jagorancin asusun a lokaci mai tsauri

A ranar Jumma'an nan an sake zabar shugabar Asusun bada Lamuni na IMF Christine Lagarde a matsayin wacce za ta sake jan ragamar wannan asusun tsawon wasu shekaru biyar da ke tafe.

Kwamitin gudanarwar asusun bisa jagorancin Aleksei Mozhin, ya bayyana Mis Lagarde a matsayin mace hazika da ta jagoranci wannan asusu da aiki tukuru a karon farko na shugabancinsa.

Mozhin dai ya yi kyakkyawan yabo ga Lagarde wacce ya ce ta riki asusun a lokacin da ake fama da matsala ta tattalin arziki a duniya amma ta yi kokari wajen ganin asusun ya bada gudunmawar da ta dace a bada shawarwari da ma tallafar kasashe da dama.